Wednesday, May 16, 2018

ZAMA CIKIN SHIRI




KO YAUSHE KA KASANCE CIKIN SHIRI

Labarin ya fara ne watanni hudu kafin shekara ta 2018, a lokacin da na yanke shawarar barin wurin aikin da nake aiki dasu domin komawa wani wurin daban. Dalilai ne masu tarin yawa a wurina da suka sanya na kudurce canjin wurin aikin.

Na yunkara na kuma gama shiri tsaf dan samarwa da kaina wannan canjin, domin kuwa har naje na tattauna da mamallakin wannan sabon wurin da zan koma, sabo ne a wurina kuma sabo ne aikace, da shi kuma ina hangen nasarata a wurin. Sai dai abinda na kasa fahimta shine; ban fa kasance cikin shiri ba kafin bayyanar da wannan kudurin daga kwakwalwata, zuciya zuwa gabbai domin aikatawa.




Zan iya farawa da rashin cikakken yanci a matsayina na ma’aikaci ya taka muhimmiyar rawa wajen kara angiza ni da kara min kaimin son canjin wurin aikin.





Na kasance mutum mai kyamar zargi, musamman akan abinda banyi ba kuma bani da ra’ayin aikata shi. Wannan ma wani abu ne da yasa na kuma kyamar tsohon wurin aikina a lokacin, dan akwai wadanda ke cuso zarge-zarge akan kowane ma’aikaci, ko da ya kasance yana aikata abin ko baiyi, sun dai yadda cewar sune masu gaskiya kuma ababen gaskatawa.

Sana’ata itace samar da shafin yanar gizo da bunkasashi (Web Design and Development) zane mai isar da sako (Graphic & Logo Design), rubuce-rubuce da gudanarwar na’ura mai kwakwalwa (Data Processing), gyara hotuna da hadawa (Photo Editing) da kuma sauran abubuwa masu alaka da wannan na’ura mai kwakwalwa.







Babban abin mamaki da kuma abinda yake bani takaici shine, kasancewar a cikin kunshin ayyukan da na lissafa a sama kadan nake aiwatarwa a wurin da nake a lokacin sakamakon su ma basu da kayyaki da kuma yanayin da ake bukata wajen da yawa daga ayyukan. Dan haka ne sai naga mai zaisa ga shi Allah Yayi min baiwa sanin fannoni da yawa amma na takaita a mafi karancin fannonin.

Da farko nayi yunkurin na zama mai aikin zaman kaina, wato nine mai gidan kaina, sai kuma na hangi abinda ka iya zuwa yazo a nawa tunanin, kamar rashin wadataccen jari, rashin isassun abokan ciniki, rashin kayan aiki da dai sauran matsaloli da kuma bukatu da suke tasowa a ma’aikatun dake amfani da na’ura mai kwakwalwa.

Sai dai kash! Rashin kasancewata cikin shiri da yunkurin yin abinnan da Bahaushe ke ce “Dare daya Allah kanyi Bature” amma ni nawa ba dare dayan yin kudi bane ko siyan babur ko mota, sai dai dare daya ne na bayyanar da fikirorina da kuma kwadayin nunawa ‘yan uwana matasa irin sana’ata domin su samu hanyar dogaro da kansu ko mai kankantarta, dan ina matukar kyamar dogaro kai tsaye da aikin gwamnati a kowane mataki.

Hakan ya sanya bayan wani dan lokaci da canjin wurin aikina, sai gani na wayi gari da tsintar kaina tsohon wurin aikin da na yiwa tawaye a baya, dalilin komarwa shine dai rashin zama cikin shirin domin kuwa ban shiryawa canjin komai ba face kwarin gwiwa da hangen samun nasara.

Hangen samun nasara tabbas abune mai sanya karsashi da bada gagarimin kwarin gwiwa wanda ka iya sanya makaho wasa a bakin rijiya.

A tunanina idan mutum (musamman matashi) ya kasance yana da wasu fikirori a cikin al’umma kamata yayi da farko dai ya zama abin alfahari, sannan kuma ayi kokarin samun hanyoyi da za a amfana da wannan fikira ko fikirori nashi domin amfanin ‘yan baya da kuma jama’ar wannan lokacin.

Dalilan da nake ganin sun kawowa manyan kasashe cigaba kenan da kuma saurin bunkasa a lokaci kadan, domin yadda da sukayi da cewa daukan masu fikira a cikin matasansu shine abun da zai taimaka masu matuka ta bangaren fatattakar zaman kawai, da rage dogaro da gwamnatoci wajen samun ayyukanyi.

Mai yasa zamu yarda mu koyar da kanmu lalaci da son jin dadin da bamu muka gina ba, lallai wannan shine yake sadar damu zuwa ga mafi yawan matsalolin da suka addabemu a wannan zamanin kamarsu; kwace, sane, fashi da makami, shaye-shayen miyagun kwayoyi wanda yanzu yake neman zama gidan kowa baga mata ba, ba kuma baga maza ba, wanda yayi mummunan rinjaye a cikin matasa.

Shin dukkan matasa ne dake shan kwayoyi ke da bukatar zuwa gidan gyaran tarbiyya? Shin mun taba damuwa da jin dalilan da suka jefa mafi yawan matasa cikin wannan halin? Na san dai mafi yawa mukan samarwa kanmu da wata amsa dake cewa abokai ne suka jefa ‘ya’yanmu, to su abokan waye ya jefa su? Shin tsakanin talauci, jahilci da rashin aiki wane ne ka iya jefa mutum cikin munanan hanyoyi?

Ya kamata mu nemi amsoshi wadannan tambayoyin.

Kamar jan irin wadannan matasa a jiki zai iya bayarda gudummawa matuka, domin ban manta ba ni ganau ne akan wani abu da ya faru tsakanin wani uba da dansa da ya afkawa wannan mummunar dabi’a.

Ya kasance kamar yadda aka fi sani yana da abokai masu irin wannan hali na shaye-shaye har shima ya kamu tun yana yi a boye har abu ya fito fili, hakanne ya tayarwa da mahaifin hankali da ganin babban dansa ya shiga wannan yanayi sannan ga darajarsa da jama’ar yankin ke gani. Anyita bashi shawarwari daban-daban, sai dai yayi dogon nazari tare da daukar shawarar wani mai kaifin hankali a cikin abokanshi kuma ma amininshi, wanda ya shawarceshi da ya ja wannan dan a jiki, ya kuma zama mai tukin motarshi tunda ya kamala karatu bai da aiki kuma; hakan kuwa akayi duk inda zaije suna tare, sannan ya ware musu lokaci domin halartar majalisun ilimin addini, cikin ikon Allah da sauran yunkuri daga iyayen wannan matashin yanzu haka ya bari kwata-kwata.

To mai zai hana kaima/kema ku jarraba irin wannan ko wasu kyawawan hanyoyi akan ‘ya’yanku da suka kangare a maimaikon gudunsu da kyararsu (amma sai idan mun kiyaye shagwabantarwa).

Haba dan uwana matashi, har sai anyi ta fama dakai akan barin shan kayan maye, kai da kake dan musulmi kuma musulmi gaba-da-baya, ga shi Ubanginka ma ya baka damarmaki da yawa dan idan ka fada tarkon shaidan ta wadannan hanyoyi ka samu tsira kamar dai yin azumi na wata guda a Ramadan, to idan har zaka iya zama wata guda kwanaki Talatin ko Ashirin da Tara ba tare da kayan maye ba ai zaka iya shanye tsawon rayuwarka ba tare da su ba.

Yanzu dan uwa idan ka kai shekarun aure ka haifi ‘danka/ki, shin zai faranta maka ace ga wancan mahaifinshi mai shan kayan maye ne; na san tabbas baza ka so hakan ba, sannan shima dan bazai so ba, karshe ma ya rika kallon ka cutar dashi.

Idan kace sai ka kara shekaru ko kayi aure sannan ka daina; waye ya tabbatar ma da zaka kara dakika guda kana numfashi, waye ya yardarma da zaka kai lokacin yin auren, kai dai zama cikin shiri ko yaushe abokina.

Tabbas zamanka cikin shiri shine kadai mafitarka, tunda idan ka waiwaya a danginka zaka kakanninka da suke kwance a kushewa sunfi wadanda ke raye nan duniya yawa, to yaya kake da tabbas din zaka kai wani lokaci mai tsawo a raye.

Ilimin addinin musulunci shine ginshiki na rayuwa kuma shine ilimin da ake cewa gishirin zaman duniya ko munki ko munso, ba kamar yadda a wannan zamanin muka dauka ba ilimin neman duniya shine komai, wai har idan anyiwa mutum magana akan yadda ya dauki ilimin addinin ‘ya’yanshi dama nashi sai yace ai da na bokonma zaka iya neman lahira.

Bamu ce baza ka iya ba, amma bazaka iya koyon sallah, azumi, hajji da sauran sassan addini a can ba, ka ga kuwa ashe da sauran gyara. Wani abin takaici wai nag a wata daliba da take a wata makarantar Islamiyya a wata unguwa da tai laifi malami ya hukuntata sai ga mahaifiyarta ta shigo da fada da maganganu marasa dadi wai an daki ‘yarta har tana fadin ai ba dole bane karatun, hmmm! Haka kuma an aika karvar kudin da ake kira Kudin Laraba sai naji iyayen na fadin wai ba aikin Allah malaman suke ba, anya kuwa wannan ilimin zai yiwa ‘ya’yan amfanin da ake bukata ko kuma dai kawai kun aika sune dan kar ace suna ‘ya’yan musulmi basu zuwa neman ilimin addinin.

Dolenmu ne ‘ya’ya da iyaye mu zama cikin shiri a dukkan lamuranmu tunda munsan bamu da tabbas idan ma muna raye akwai tsufa ko kuma rashin cikar buri wadanda dukkansu abubuwa ne zasu iya kawo mana cikas a rayuwarmu ta yau da kullum ko mun sani ko bamu sani ba. Aikin dai namu ne dukanmu sai mun yarda da cewar dukkan ‘ya’ya namu ne babu wata wariya ko bambanci domin wata ranar ba dan da mukai raino bane zai amfanemu

Matsalolin sun fi karfin a fade su a rubutu daya, amma suna nan da yawa a sauran rubuce-rubucenmu a wannan shafi domin bayarda gudummawa ta fuskar da zamu iya.

Hamza Ahmad Fagge

No comments:

Post a Comment

Give us Feedback